Matar ta bayyana yadda ta haihu a asibiti ba tare da tasan tana ɗauke da Juna 2 ba

Matar ta bayyana yadda ta haihu a asibiti ba tare da tasan tana ɗauke da Juna 2 ba

Wata mata ta bayyana yadda ta je asibiti don neman maganin ciwon ciki amma a karshe ta haifi ‘yarta jaririya.

Matar mai suna Favour ta ce ta fara fuskantar yawan kiba yayin da daga bisani ta koma kawadayin komai da ta gani


Mutane da dama sun yi martani inda su ke cewa yanzu ana yawan samun irin wannan juna biyun a jikin mata
Wata mata ‘yar Najeriya mai suna Favour Ehizibue ta bayyana yadda ta gamu da juna biyu mai dauke da abin al’ajabi.

Matar ta yada faifan bidiyo a TikTok inda ta ce ta je asibiti neman maganin ciwon ciki amma abin mamaki ta dawo gida da jaririya.

Mata ta haihu a asibit ba tare da sanin da ta na dauke da ciki ba
Wata mata ta bayyana yadda ta haihu ba tare da ta san ta na ciki ba.

Hoto: @favourofafrica_. Asali: TikTok
Favour ta ce bata taba sanin ta na da juna biyu ba lokaci daya kawai ta ga alamun ta na kara kiba wanda hakan ya saka ta yi murna.

Yawan kiban nata ya saka ta na jin kwadayin abubuwa inda ta ke fama da kumburar fuska ta dauka cewa kawai matsalar fatar jiki ce, Legit ta tattaro.

Ta ce a karshe, ta yi fama da ciwon ciki wanda duk a daukanta magani kawai ta ke bukata amma da zuwanta asibiti sai aka shigar da ita dakin haihuwa.

Views: 240

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *