NDLEA ta kama hodar-iblis da aka ɓoye cikin littattafan addini za a kai Saudiya

NDLEA ta kama hodar-iblis da aka ɓoye cikin littattafan addini za a kai su Saudiya

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA sun cafke hodar iblis da aka boye a cikin littafan addini guda 20 da ake niyyar zuwa kasar Saudiyya da su.

Sanarwar da kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ya fitar ta ce an gano hodar Iblis din mai kunshe da dauri 20, mai nauyin giram 500 a cikin kwalin litattafan addini a ranar Talata 15 ga watan Afrilu.

Ya ce jami’an na NDLEA na sashin ayyuka da bincike na kasa, DOGI, ne su ka gano haramtaccen kayan a lokacin da su ke binciken kayan da ake fitarwa zuwa Saudi Arabiya a kamfanin hada magunguna.

Views: 6710

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *