Rikicin siyasa ya ɓarke tsakanin Rarara da Mansura Isa Mansura Isa ta yiwa Rarara wankin babban bargo inda ta tsine masa tare da cewa baya kishin Arewa

Rikicin kalaman siyasa tsakanin yan Kannywood da mawakan siyasa ya sake barkewa bayan tsohuwar jarumar fim kuma tsohuwar matar Sani Danja, Mansura Isa ta fito fili ta yiwa fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara wankin babban bargo.
Rikicin siyasa ya ɓarke tsakanin Rarara da Mansura Isa
Mansura Isa wacce aka sani da fada a ji a duk lokacin da lamarin ya shafi talakawa, ta bayyana a wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok da Facebook inda ta nuna bacin ranta matuka kan yadda Rarara ya ci gaba da rera wakokin yabon Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsanancin halin rayuwa.
Me Mansura Isa ta ce wa Rarara?
Rikicin siyasa ya ɓarke tsakanin Rarara da Mansura Isa
A cikin bidiyon wanda yanzu haka ya karade soshiyal midiya, Mansura Isa ta yi magana cikin fushi da bakin ciki. Ta ce ita mamaki ne take yi yadda Rarara wanda ya fito daga Arewa kuma ya san halin da talakawan Arewa ke ciki, zai rufe idonsa ya ci gaba da wakar goyon bayan gwamnati.
Rikicin siyasa ya ɓarke tsakanin Rarara da Mansura Isa
Ta ce, “Rarara wallahi baka kishin Arewa. Baka kishin talaka. Duk abinda ka sani shine kudi. Idan an baka kudin ka zaka manta da kowa. Yau talaka baya iya sayen buhun shinkafa, man fetur ya tashi sama, yara basu zuwa makaranta saboda yunwa, amma kai kana can kana waka ‘Sai Tinubu’. Wannan wakar taka don kudi ce ba don kishin kasa ba.”
Rikicin siyasa ya ɓarke tsakanin Rarara da Mansura Isa
Mansura ta kara da cewa aikin mawaki a gargajiyance ba wai yabo kawai ba ne, gyara ne. Ta ce da can mawaka irinsu Mamman Shata da Dankwairo sun rera waka ne domin su fadi gaskiya ga shugabanni, ba domin su karbi kudi su rufe bakinsu ba.
Ta tsine masa da cewa idan har bai daina yaudarar talakawa da waka ba, to tarihin Arewa ba zai manta da shi da kyau ba. Ta ce Allah zai tambaye shi akan bakin da yake amfani da shi wajen rufe gaskiya.
Dalilin da yasa Mansura ta fusata
Ba wannan ne karon farko da Mansura Isa ke nuna goyon bayanta ga talakawa ba. A baya ma ta taba fashewa da kuka a wani bidiyo tana magana akan halin da yayan talakawa ke ciki a Arewa. Ita mutun ce mai kishin Arewa kwarai da gaske, kuma ta sha fada a ji akan cewa yan Kannywood da mawaka su daina sayar da Arewa saboda kudi.
A cewarta, Rarara wanda gwamnatin APC ta yi amfani da shi sosai a lokacin yakin neman zaben 2023, ya kamata yanzu ya yi shiru ko ya yi amfani da muryarsa wajen isar da kuken talakawa ga Shugaba Tinubu, maimakon ya ci gaba da rera wakokin cewa komai yayi kyau alhalin komai na kara tabarbarewa.
Ta ce, “Idan an baka kudi ka ci, ka ci, amma kar ka zo ka rera waka ka ce talaka na farin ciki. Talaka na kuka. Ka fito ka ji kukan jama’a.”
Martanin jama’a a soshiyal midiya
Bayan bidiyon ya fita, mutane sun rabu gida biyu. Wasu da dama musamman matasa a TikTok da Facebook sun cika comment da cewa “Mansura ta fadi gaskiya”. Suna cewa Rarara da sauran mawakan siyasa sun ci amanar talaka, sun karbi kudi sun manta da talaka.
Wani mai amfani da Facebook ya rubuta, “Mansura Isa ta yi abinda ya kamata. Rarara baya kishin Arewa, kawai abin aljihunsa ya sani.”
A daya bangaren kuma, magoya bayan Rarara musamman wadanda ke cikin kungiyar APC sun fito suna kare shi. Suna cewa Rarara dan kasa ne mai kishin kasa, kuma yana da hakkin ya goyi bayan shugaban da yake so. Suna cewa Mansura Isa bata da hurumin ta tsine masa saboda ra’ayinsa na siyasa.
Har zuwa yanzu dai Rarara bai mayar da martani ba game da wannan zargi da Mansura ta yi masa.
Shin Rarara baya kishin Arewa da gaske?
Wannan tambayar ce ta zama babbar magana a Arewa. Rarara dai shi ne mawaki mafi tasiri a siyasar Arewa a shekarun nan. Wakokinsa na siyasa sun taka rawa sosai wajen lashe zabe a 2015 da 2019 da 2023. Amma kuma masu suka suna ganin yanzu lokaci ya yi da ya kamata ya yi amfani da wannan tasirin nasa wajen fadawa gwamnati gaskiya, ba yabo kawai ba.
Mansura Isa a nata bangaren ta ce ba za ta yi shiru ba muddin ana cutar talaka ana kuma biyan mawaka kudi su rera karya.
Wannan dai ba shine karon farko da aka yi irin wannan arangama tsakanin jarumai da mawaka ba. Amma wannan karo ya fi zafi saboda Mansura ta yi magana da tsantsar zafin zuciya har ta kai ga tsinewa.
Shin kuna goyon bayan Mansura Isa ko kuna ganin Rarara bai yi laifi ba? Ku bayyana ra’ayinku a kasa.
Views: 4
