Dalilin da yasa Adam A Zango ya saki matrsa ta 6 Maimuna Pretty

Dalilin da yasa Adam A Zango ya saki matarsa ta 6 Maimuna Pretty da kuma jerin matan daya aura.

Da asubahin ranar Alhamis, masoyan fina-finan Hausa sun farka da wani labari mai tayar da hankali wanda ya karade kafafen sada zumunta kamar wuta a cikin daji. Labarin dai shine, fitaccen jarumi kuma mawaki, Prince Adam A. Zango ya saki matarsa ta shida, jaruma Salamatu Maimuna Musa, wacce aka fi sani da Maimuna Pretty ko kuma Maimuna Garwashi.

Dalilin da yasa Adam A Zango ya saki matarsa ta 6

Auren nasu wanda aka yi a asirce a Jihar Kebbi a tsakiyar watan Agustan shekarar 2025, wanda kowa ke ganin kamar zai zama aure na karshe da zai kawo karshen dogon zangon neman zaman lafiya na Zango, ya kare cikin kasa da shekara guda.

Dalilin da yasa Adam A Zango ya saki matarsa ta 6

https://hausa.legit.ng/kannywood/1722521-adam-a-zango-ya-saki-matarsa-maimuna-pretty-fara-kwashe-kayanta

Majiyoyi na kusa da gidan jarumin a Kaduna sun tabbatar da cewa, tun kwanaki uku da suka wuce aka fara ganin alamun tashin hankali a gidan. Wata makwabciyarsu da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce, “Mun dade muna jin hayaniya da rigima, amma bamu taba tunanin har abin zai kai ga saki ba. Jiya da daddare sai muka ga motar daukar kaya ta shigo gidan Zango. Da safe muka ga ana kwashe gado, kujeru, firinji da kuma manyan akwatuna zuwa wata mota kirar Hilux da aka ce zata wuce gidan iyayen Maimuna a cikin Garin Kebbi.”

Dalilin da yasa Adam A Zango ya saki matarsa ta 6

apahausa.com.ng

Wani abokin Zango na kut-da-kut wanda yake aiki a karkashin kamfaninsa na White House Family Productions ya kara da cewa, rikicin ya samo asali ne daga rashin fahimtar juna da kuma shiga tsakanin masoya daga waje.

Dalilin da yasa Adam A Zango ya saki matarsa ta 6

An ce Adam Zango mutum ne mai son zaman lafiya da kuma tsananin kishi, yayin da Maimuna kuma sabuwar jaruma ce da take son ci gaba da fitowa a fina-finai. An ce wannan ne ya haddasa sabani. Jarumin yana so ta rage fitowa a wasu shirye-shiryen da yake ganin basu dace ba, ita kuma tana ganin ya kamata ya bata dama ta gina sana’arta.

Har ila yau, wata majiya ta dora laifin a kan matsin lamba na kafafen sada zumunta. Tun bayan aurensu, mutane da yawa sun rika cewa “wannan auren ma bazai jima ba kamar sauran”, wanda hakan ya sanya Maimuna cikin damuwa da fargaba kullum. Duk kalaman soyayya da Zango yake yawan yi mata a Instagram suna cewa “My last bus stop”, sai ta rika ganin kamar wasa.

Zuwa yanzu dai, babu wani kalami a hukumance daga bakin Adam Zango ko Maimuna Pretty. Dukkaninsu sun yi shiru, sun kuma kashe layin wayoyinsu. Shafin Instagram na Zango wanda kullum yake cike da bidiyoyi, ya yi shiru tun kwana biyu. Ita ma Maimuna ta goge dukkan hotunan aurenta da Zango a shafinta, ta bar daya tilo na ranar da aka daura mata aure, wanda hakan ya kara tabbatar wa duniya cewa lamarin gaskiya ne.

Masoya da dama sun bayyana alhininsu. Wasu na cewa, “Allah ya kyauta, Zango jarumi ne na kwarai amma matsalar aurensa ta yi yawa.” Wasu kuma na ganin cewa jarumar ce ta gagara hakuri da halin mawaki mai son zaman kansa.

Ana dai kwashe komatsenta zuwa gidan iyayenta a hankali, kamar yadda al’adar Hausawa ta ce idan aka saki mace. An ce da zarar an gama kwashe kayan, za a aika da takardar saki ta hannun wani babba a masarautar Zango.

Wannan lamarin ya sake bude tsohuwar raunuka a zukatan masoyan Zango, domin kowa na addu’ar Allah ya bashi zaman lafiya a rayuwar aure.
ADADIN MATAN DA ADAM A. ZANGO YA TABA AURA KUMA YA SAKE SU
Wannan ba shine karon farko da Adam A. Zango yake fuskantar rabuwar aure ba. A tarihin rayuwarsa, masana Kannywood da kafafen yada labarai sun tabbatar da cewa ya yi aure akalla sau shida kafin Maimuna, kuma mafi yawansu sun kare da saki.

Ga jerin sunayen matan da Adam A Zango ya taɓa aura

Amina – Matar Fari (2006): Ita ce budurwarsa ta farko. Ya aure ta a shekarar 2006 lokacin yana da shekaru 20. Ta haifa masa dansa na fari, Haidar. Aurensu ya rabu bayan shekaru kadan, watanni biyar bayan haihuwar dansu.

Aisha – Ta Biyu (2009): Bayan rabuwa da Amina, ya auri wata budurwa mai suna Aisha a 2009. Wannan ma bai jima ba ya rabu.

Maryam – Ta Uku: Wata ‘yar jihar Nasarawa ce mai suna Maryam. Ita ma aurensu ya kare da saki.

Maryam Abdullahi Yola – Ta Hudu (2013): Wannan ita ce fitacciyar jaruma Maryam Yola. Sun hadu a shirin film din “Nas” kuma suka yi aure a Lugbe, Abuja a 2013. Wannan auren ma ya mutuwar ya mutu.

Sadiya Umar Chalawa / Safiyya Umar Chalawa – Ta Biyar: Wannan auren ya fi daukar hankali. An ce rabuwarsu da ita ce ta saka Zango har ya shiga damuwa (depression) a shekarar 2024, har ya fito ya bayyana a bainar jama’a cewa yana fama da damuwa saboda sakinta. Wasu rahotanni sun ce wannan ita ce matarsa da aka saki a 2023.

Maimuna Musa (Maimuna Pretty) – Ta Shida (2025): Ita ce ta karshe da ya aura a asirce a Kebbi a ranar 15 ga Agusta, 2025, wacce yanzu labarin sakinta ke yawo.

A takaice, kafin Maimuna, Adam A. Zango ya taba yin aure sau biyar kuma ya sake su, kuma ya haifi ‘ya’ya shida – maza hudu da mata biyu daga cikinsu. Idan har labarin sakinta na yanzu ya tabbata, to adadin matan da ya aura kuma ya sake su zai kai shida kenan.

Shi kansa Zango a wani lokaci ya taba bayyana cewa yana fargabar sake yin aure saboda “rashin biyayya” da ya ke gani daga matansa na baya.

Allah dai ya kawo mafita, kuma ya bawa Adam Zango da Maimuna Pretty hakurin jure wannan jarabawa.

Views: 1

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *