Yadda wani soja ya yi min cikin shege ya tsere—Comfort

Wani sojan Najeriya ya ɗirkawa yarinya mai shekaru 19 ciki a jihar Bauchi sannan kuma ya tsere.

Sojan Najeriya Ya Ɗirkawa Yarinya Mai Shekaru 19 Ciki a Bauchi Ya Tsere

Matashiyar mai suna Comfort Peter wadda a yanzu ke da shekaru 23 ta bayyana cewa a shekarar 2017 ne sojan mai suna Julius Simon ya ɗirka mata ciki.

Ta roƙi hukumar sojojin Najeriya da ta nemo mata masoyin nata.

Tace sojan ya mata fyaɗe tana ƴar shekaru 19 wanda hakan ya kai ga ta ɗauki ciki.

Labarin nata mai cike da abin tausayi, tace sojan ya gayawa babanta cewa zai aureta amma baban nata na son ta yi karatu dan haka ne ma ya ce ta zaɓi karatu ko aure inda tace masa aure take so.

“Sojan ya gayyace ni ɗakinsa inda da farko na ƙi zuwa amma yace min sun gama aiki ne zasu koma Biu dan haka yake son ganina.”

“Haka nan naje ta sameshi, amma sai ya hanani komawa gida yace dole in kwana a wajensa. Na gaya masa cewa babana zai dokeni amma ya hanani komawa gida ya kwace wayata inda yace min ai aurena zai yi.”

“Dole na kwana a wajensa kuma ya min fyaɗe. Da na koma gida sai da babana ya dokeni kamar zai kashe Ni.”

“Bayan kwana biyu na fara amai inda mahaifiyata tace malaria ce, sai dai daga baya sai ciki ya bayyana.”

“Mun riƙa zuwa wajen sojan amma sai ya riƙa ce min ba zai aureni ba, in tafi in bashi waje.”

“Yanzu ɗansa ya kai shekaru 2 kuma yana tambayar mahaifinsa, dan haka ya zo ya ɗauki ɗansa kawai shine abinda nake nema.” Inji Comfort.

©Idonmikiya.

Views: 16

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *