Fitaccen malamin addinin Islamar nan da yayi suna wajen jawo ce-ce-ku-ce malam Bello Yabo na jihar Sokoto ya yi wani wa’azi mai ratsa jiki wanda mutane da dama su ka dinga cece-kuce akansa.
A wani bidiyo wanda shafin Northern Nigeria Bleeds su ka wallafa Facebook, fitaccen Malamin ya bai wa ‘yan Najeriya shawarar mallakar bindiga.
A cewar Malam Bello Yabo, yadda harkar tsaro ta tabarbare a kasar nan, ya kamata ko wanne dan Najeriya ya nemi duk inda ‘yan bindiga su ke zuwa siyo makamai ya siya.
Views: 16
