Limamin Ka’abah ya shiga harkar fim a Saudiyya

Kamar yadda shafin Labarun Hausa ya ruwaito cewa.

A cikin wani gajeren bidiyo mai tsawon minti biyu, tsohon Limamin Ka’aba, Sheikh Adil Al-Kalbani, ya bayyana takaitaccen bayani kan matsayar shi.

Wani hoton fim mai dogon zango mai suna “Combat Field” da aka dauka a birnin Riyadh a cikin wannan shekarar ta 2021, zai nuna tsohon Limamin Masallacin Ka’aba, Sheikh Adil bin Salem bin Saeed Al-Kalbani.

LOKACIN DA YAKE LIMANCI A KA’ABAH

Lamarin dai ya jawo maganganu masu yawan gaske a shafukan sada zumunta na zamani, inda aka dinga caccakar tsohon Limamin da maganganu kala-kala.

Sheikh Adil Al-Kalbani ya fito a cikin wani na talla da aka nuno dakarun sojoji a filin daga dauke da makaman yaki. Bidiyon mai tsawon minti 2 da dakika 41 ya nuna tsohon Limamin Ka’abar kuru-kuru a ciki.

Shafin Twitter na hukumar jin dadi da nishadi ta kasar Saudiyya sune suka wallafa wannan bidiyo a shafinsu mai suna Turki Alalshikh

© Labarun Hausa

Views: 12

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *