
Wasu rahotanni daga jihar Sokoto waɗanda bamu kammala tantance sahihancinsu ba na cewa an kama malamin addinin Islamar nan Murtala Assada kan wasu kalamai da yayi game da sha’anin tsaro.
Kawo yanzu dai sashin Hausa na APA bai kammala tabbatar da gaskiyar rahotannin ba amma kuma shafin Sokoto Online ya ruwaito cewa.
Wasu magoya bayan Gwamna Tambuwal sun nemi Gwamna Tambuwal da ya kama Malam Murtala Assada kan tonon sililin da ya yi kan matsalar tsaro.
Wasu magoya bayan Gwamna Tambuwal sun bukaci Gwamna Tambuwal da ya kama shahararren Malamin addinin musulunci a jihar Sokoto Sheikh Malam Murtala Assada kan irin yadda yake sukar Gwamna akan matsalar tsaro.
A cikin wani wa’azi da Malamin ya gabatar, Sheikh Murtala ya bankoda yadda Gwamnatin jihar Sokoto ta bai wa ‘yan bindiga su Bello Turji kudi domin bari a gudanar zabe a yankunan Sabon Birni.
A cikin wa’azin Malamin, Sheikh Murtala ya ce idan karya ne a gayyace shi yana da hujjoji akan abin da ya fada.
Wadannan kalamai na Malam ba su yi wa magoya bayan Gwamna Tambuwal dadi ba, inda har su ka bukaci da Gwamna ya kama shi.
Shin meye ra’ayin ku akan wannan ne?
©Sokoto Online
Views: 21
