Yadda Sarkin Daura mai shekaru 90 ya auri budurwa ƴar shekara 20

Sarkin Daura, Umar Faruq Umar, Mai Shekaru 90, Ya Auri Budurwa ‘Yar Shekara 20 A Katsina.

Hoton Amarya

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar Ya Angwance a Ranar Asabar Din Da Ta Gabata A Cikin Garin Katsina.

Majiyar Blueink News Hausa Ta Nakalto Cewa Sarkin Wanda Ke Da Shekara Kusan 90 A Duniya Ya Auri Amaryarsa Mai Suna Aisha Iro Maikano.

Majiyar Ta Tabbatar Da Cewa Shekarunta 20 A Duniya. Har Ila Yau, Majiyar Ta Gano Cewa Mai Martaba Ya Biya Sadakin Zunzurutun Kuɗi Har Naira Miliyan Daya Nan Take, Amaryar Yar Gidan Fagachin Katsina Ce, Hakimin Matazu A Jihar Katsina.

Majiyar Blueink News Hausa Ta Shaida Mata Cewa An Daura Auren A Cikin Garin Katsina A Wani Dan Kwarya-kwaryar Taro, Watau Babu Mutane Da Yawa.

Allah Ya Ba Da Zaman Lafiya Da Zuri’a Dayyaba!

Views: 50

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *