Dalilan da suka sa na ce ba zan taɓa yin sulhu da Kwankwaso ba—Ali Baba

SIYASAR KANO | Bazan Taba Yin Sulhu Da Kwankwaso Ba, Cewar Ali Baba.

Daga Comr Nura Siniya.

Mai baiwa Gwamnan kano shawara kan al’amurran addini Ali Baba Agama lafiya Fagge ya ce har abada ba zai kara bin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a siyasa ba, har sai ranar da yai mashi ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarshi kuma yai mata addu’a, kamar yadda ya fada a cikin wata fira da aka yi dashi a gidan Rediyon Freedom da ke jihar kano.

Ali Baba, ya ce ko Gwamnan kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yai sulhu da kwankwaso shi ba zai taba yin sulhu dashi ba.

A cikin zantawar Ali Baba, ya bada sharadin cewa ba zai taba yi ma Ganduje biyayya ba matsawar ya nemi tursasashi akan cewa lalle dole sai ya sulhunta da kwankwaso indai har bai yi mashi ta’aziyyar mahaifiyarshi ba.

Masu karatu ya kuke kallon wannan batu?

Views: 40

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *