Nan ba da daɗewa ba gaba ɗaya Duniya za ta zama ƙasar Musulunci in ji Babban Paston Cocin kasar Rasha

Nan bada dadewa ba gaba daya Duniya zata zama kasar musulunci.
Inji – Babban Paston Cocin kasar Rasha

Acewar shugaban cocin Rasha, Kasashen Turai irin su kasar Rasha da sauran Kasashen yammacin Turai duk sun fara zama kasar musulunci, saboda a kasar Jamus Kashi
30% cikin dari na kiristocin kasar duk tsofaffine. Hakan yasa kashi 70% na matasa masu jini a jika na Jama’ar kasar zasu zama musulmi Nan bada dadewa ba.

Paston yaci gaba da cewa, akasar shi ta Rasha, kiristoci suna cike filayen kwallo da gidanjen rawar Disco, amma a ranakun lahadi sai kaga babu kowa a coci. Amma a gefe daya musulmai suna cika masallatai don gunar da ibada.

Abun mamaki ne yadda dubban musulmi sukeyin dandazo a manyan filayen wasanni don gudanar da sallalolin idi, wannan ba karamin abun mamaki bane.

Duk inda ka shiga a kasar Ingila, zakaji Ana ta ambaton sunan annabi Muhammad.

Sannan a halin yanzu Kaso 49% na mazauna birnin Brussels duk Muslmi ne. Don haka nake Kara jaddadawa nan bada jimawa ba duk Duniya zata zama kasar musulunci.

Views: 21

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *