Sunansa Usman Shugaba dogarin Aisha Buhari wanda ake zargi da kama Aminu Muhammad

Hoton Aisha Buhari da Aminu Muhammad

A farkon wannan makon da muke ciki ne dai kafafen watsa labaran duniya waɗannan suka haɗa da na cikin gida da waje, da shafukan yanar gizo.

Suka cika maƙil da labarin wani matashi da ke karatu a Jami’a, mai suna Aminu Muhammad wanda ake zargin yayi wani rubutu a shafinsa na Twitter inda ya zargi uwar gidan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Aisha Buhari.

Da cewa “Su mama an ci kuɗin talakawa an ƙoshi” ga hoton Screenshot ɗin abinds ya rubuta a shafin nasa na Twitter.

An dai yi zargin cewa wani jami’in tsaro mai suna Usman Shugaba dogarin Aisha Buhari ne ya jagoranci kama matashin, duk da cewa babu wata shaidar dake gasgata zargin wanda wani mai amfsni da shafin Twitter mai suna Dr. Dabo ya wallafa.

Views: 17

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *