Kamar yadda kuka sani mafarki wani abu ne mai ban al’ajabi saboda wani lokacin idan akace ka yi shi yana iya tabbata gaskiya domin za ka iya ganin abin a zahiri ya faru wato zaka iya ganin faruwar abinda kayi mafarki a zahiri.
Yayin da a wani lokacin yaka zamo ƙanzon kurage komai dai inda mafi yawan mafarke mafarken da al’umma ke yi a yayin da suke gudanar da bacci ƙarya ne ba gaskiya ba.
A nan wata budurwa ce ta bayyana wa Duniya cewa ita fa ta yi mafarkin cewa ta auri Shugaban Najeriya Muhammadu aure irin na Sunna, budurwar mai suna Fatima Ta bayyana haka ne a shafin ta na Facebook
A wani labarin kuma.
Dangane da ƴar hatsaniya ko tarzomar da aka samu a ranar jiya Juma’a a unguwar Tudun Yola rahotanni sun bayyana cewa a safiyar yau asabar
Al’amura sun soma komawa daidai a unguwar Tudun Yola da ke Kano.
Rikicin jagoranci ya tilasta rashin yin sallar Jumu’a a Masallacin Darul Hadith na marigayi Dr. Ahmad Ibrahim BUK.
Tarzoma ta kaure a Masallacin ne lokacin da sabon liman zai hau Mumbari don soma huɗu ba, inda wasu fusatattu suka janyo rigarsa ta baya don nuna ƙin amincewa da shi, lamarin da ya kawo rikici.
Tuni aka rufe masallacin tare da baza jami’an tsaro a kofa da kewayensa domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya.
Yanzu haka dai tuni ɓangarorin biyu suka nufi shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai domin sasantawa.
Muna tare da ƙarin bayani nan gaba.
Views: 42
