Da Ɗumi Ɗumi: “Za ayi dare biyu a ranar Talata a wasu ƙasashen Duniya ciki harda Najeriya”—NASA

Hukumar binciken sararin samaniya ta ƙasar Amurka Nasa tace za’ayi dare biyu a yankunan Duniya daban daban yankunan sun haɗa da Nahiyar Turai, Asia, Pacific, Latin, Afrika waɗannan yankuna zasu haɗu da mummunan duhu da misalin ƙarfe 11:00AM na rana a agogon ko wace hahiya.

A wasu yankunan duhun zai ɗauki tsawon mintuna 45-50 kafin gari ya sake wayewa, daga cikin ƙasashen da lamarin zan shafa sun haɗa da Najeriya Nijer, Cameroon,Chad Malawi, Morocco, da jamhuriyar Benin da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya NASA ta ce ranar Talata mai zuwa za’a fuskanci duhun ranar.

Wannan sanarwa ta hukumar NASA ta fito ne a shafin jaridun Daily da Telegram.

A wani labarin kuma

Buhari Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Aishatu Ahmad Binani A Yola

Daga Babayi Mohammed Arabo

Da ranar wannan litinin din ne dai dubban magoya bayan jamiyyar APC suka fito kwansu da kwarkwata domin kaddamar da mace daya tilo daga arewacin Najeriya wacce take takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jamiyya mai mulkin Najeriya APC

Taron wanda ya samu halartar Shugaba Buhari na Najeriya da dan takarar shugabancin kasar karkashin jamiyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Ahmad Tinubu da shugaban jamiyyar na kasa Abdullahi Adamu da sauran kusoshin jamiyyar a mataki na kasa da tsohon gwamnan jihar Adamawa Vice Admiral Murtala Hammayero Nyako da jiga jigan jamiyyar a jihar Adamawa

Dubban mata ne dai suka halarci wannan gangami kuma daya daga cikinsu ta shaidawa Zuma Times cewa wannan bikin nasu ne kuma suna da yakinin cewa zasu kafa tarihi a karon farko

Da yake jawabi a wajan taron dan takarar shugabancin kasa a jamiyyar Bola Ahmad Tinubu yace a zabi Binani domin zata kawowa jihar Adamawa duk abinda suke bukata na more rayuwa

Itama a nata bangaren Aishatu Binani tace wannan dama da suka samu ya nuna cewa mata zasu iya taka duk wani rawa a siyasar Najeriya ba tare da kowace irin matsala ba

Taron wanda ya gudana cikin tsauraran matakan tsaro a filin taro na Muhammadu Buhari dake Yola fadar jihar Adamawa an kammalashi lami lafiya.

©️Zuma Times Hausa

Views: 67

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *