Sheikh Ɗahiru Bauchi ba lafiya yana buƙatar addu’o’i ga ƴan uwa Musulmin Duniya

Shahararren malamin addinin Islama a Najeriya Sheikh Ɗahiru Bauchi na bukatar addu’o’in ƴan’uwa musulmin da fatan Allah ya ƙara masa lafiya.

A shekarar 2018, an yi ƙiyasin akwai mutane miliyan 60 da ba su da ruwan sha mai kyau a Najeriya. Wannan ƙiyasin ya kusa yawan mutanen United Kingdom ya kuma fi na South Africa da ma wasu ƙasahen yawa.

Amma abun takaici, a shekarar 2022, wasu gwamnoni a Najeriya sun kashe kuɗi wajen miliyan 100 don siyan fama-famai na takarar shugaban ƙasa. Sun yi haka kuwa duk da sun san ko zaɓukan fidda gwani (primary elections) ba za su ci ba.

Ɗan jarida kuma marubuci Simon Kolawole ya ce, idan za a gina rijiyar tuƙatuƙa (borehole) duk ɗaya a N500,000, miliyan 100 za su gina guda 200. Saboda Allah mutum nawa (daga miliyan 60 ɗin can) za a samar wa ruwan sha mai kyau? Rashin lafiya nawa za a kawar?

Abun haushi, shugabanni ba su damu da lafiyar jama’ar da suke mulka ba. Idan ba su da lafiya, ko da mura ce kuwa, ƙasar waje suke tafiya. Idan kuwa suna buƙatar taimakon gaggawa, a asibitin kuɗin da ya fi kowanne tsada da kyau za a duba su. Sun dai iya siyasa da wasa da hankalin talaka.

Allah ya iya mana kawai, amin.

Muhsin

NB: Na hakaito wannan rubutun daga littafin Simon Kolawole mai suna “Fellow Nigerians, It’s All Politics: Perspectives On The Nigerian Project”.

Views: 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *