Ƴammata 2 sun ba hammata iska yayin da suka haɗama saurayi 1 Shagalin ranar haihuwa

Wata budurwa ta labarta yadda ta so ba saurayin ta mamaki ranar zagayowar haihuwarsa ta hanya kawo masa kyautuka da dauko masa masu busa algaita.


Ga mamakinta, ta iske wata budurwa a gidansa tana shirya masa sha tara ta arizki, wanda hakan ya janyo suka ba hammata iska.


Hakan ya yi sanadin samun raunin daya daga cikin masu busa sarewar, inda daga bisani biyun suka gane yaudararsu ya ke.


Wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna Juwon ta labarta yadda aka ba hammata iska ranar zagayowar haihuwar saurayinta yayin da ta iske shi tare da wata budurwa.

Budurwar mai shekaru 21 ta bayyana yadda ta shirya wa saurayin nata bikin zagayowar ranar haihuwarsa a matsayin ba-zata inda ta yi hayar mai busa algaita da kyautuka, ga mamakinta ta iske wata budurwa a gidan shi tana shirya mishi irin abun da ta shirya.

Take a nan ‘yan matan suka kwashi dambe a gidansa, wanda ya yi sanadiyyar samun raunin daya daga cikin masu busa algaitar da suka zo da su.

Abun mamaki shi ne yadda suka gano babu wacce yake so da gaske a cikin su biyun.

Source: hausa. legit.ng

Views: 33

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *