VIDEO: Yadda wani matashi mara hannuwa ya ƙware wajen iya ɗinki
Wani matashi musaki mara hannuwa ya ƙi yarda zuciyar sa ta mutu, inda yaje ya koyi sana’ar ɗinki.
A wani bidiyo da ya yaɗu a TikTok, yana nuna yadda matashin yake sarrafa keken ɗinki cikin ƙwarewa
Bidiyon ya nuna cewa matashin baya da hannuwa inda suka yi kama da gundulmi alamar kamar an yanke su.
Wani matashi mara hannuwa yasha yabo sosai a TikTok saboda yadda ya dage ya zama ƙwararren tela, domin cin gashin kansa.
A wani bidiyo da @saubekandeumw ya sanya, ya nuna matashin yana da gundulmin hannu domin hannuwan sa sun yi kama da an yanke su daga wuyan hannu.
ku latsa nan domin ganin Bidiyon tela👇👇👇👇👇👇👇
Jajircewar sa wajen ganin ya nemi na kan sa duk da halin da yake ciki ya sanya yasha yabo sosai a wajen masu amfani da TikTok.
Duk da rashin hannun sa ya sanya zare cikin allura
Duk da ƙanƙantar da allura take da ita, sai da matashin ya sanya zare a cikin ta ba tare da amfani da hannuwan sa ba.
Bayan ya samu nasarar yin hakan, sai ya fara ɗinka kayan inda yake amfani da hannun sa wajen daidaita kayan a saman keken dinkin.
Ƙwarewar sa wajen ɗinkin da kuma jajircewar da yake da ita na ganin ya tashi yayi ya samu na kanshi, ya burge mutane sosai a TikTok.
Source: legit.ng.hausa
Views: 16
