Ashe haka maza suke ji: Wata Budurwa ta mika ƙoƙon soyayyarta ga Saurayi yace baya yi

“Haka Maza Ma Suke Ji”: Budurwa Ta Mika Kokon Soyayyarta Ga Saurayi, Ya Ce Baya Yi

Wata matashiya yar Najeriya wacce ta fada tarkon soyayyar wani gaye ta tona masa sirrin da ke zuciyarta amma sai ya ki amsar tayinta
A wani sakon murya ta WhatsAPP, yarinyar ta ce tana ta boye soyayyar da take yi ma gayen na tsawon lokaci


Da ta bayyanawa saurayin sirrin da ke zuciyarta, sai ya ki karbar soyayyarta cikin wani siga mai ban dariya
Wani sakon murya na wata budurwa da ke mika kokon soyayyarta ga wani saurayi ya sa mutane da dama tofa albarkacin bakunansu.

A hirar tasu, yarinyar ta bayyanawa mutumin yadda take jin soyayyarsa a zuciyarta, tana mai nuna cewa so take su kulla alaka a tsakaninsu.

Budurwa da hirarsu da wani saurayi
“Haka Maza Ma Suke Ji”: Budurwa Ta Mika Kokon Soyayyarta Ga Saurayi, Ya Ce Baya Yi .

Ya ki amsa tayinta da waka
Matashiyar tana boye soyayyar da take yi wa saurayin na tsawon lokaci don haka take so ta sanar da shi ko za a dace shima yana jin ta a zuciyarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Saurayin wanda baya jin ta a zuciyarsa ya yi watsi da tayin da ta yi masa ta hanyar tura mata shahararriyar wakar nan na sabulun opera a Najeriya.

Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka yi martani ga bidiyon sun ce wannan ne dalilin da yasa mata basa son furta soyayyarsu ga maza.

Source:hausa.legit.ng

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *