An yankewa wani wakilin Opay Rabi’u Isah Gaida hukuncin daurin watanni tara a gidan yari

An gurfanar da shi a gaban kotun Shari’a bisa zarginsa da laifin damfarar N300,000 mallakar wani Zubairu Murtala ta hanyar banki ta yanar gizo.

An yankewa wani wakilin Opay Rabi’u Isah Gaida hukuncin daurin watanni tara a gidan yari.

Wata kotun shari’a ta Kano da ke zamanta a Kwana Hudu ta yanke masa hukuncin dauri a ranar Juma’a.

An gurfanar da shi a gaban kotun Shari’a bisa zarginsa da laifin damfarar N300,000 mallakar wani Zubairu Murtala ta hanyar banki ta yanar gizo.

Dan sanda mai shigar da kara, Aliyu Abidin, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin (Zubairu) ya yi korafin cewa wanda ake kara ya sace masa kudi Naira 300,000 ta hanyar yin musayar kudi ta yanar gizo ba tare da izininsa ba a lokacin da ya ba shi wayarsa ya bude masa asusun ajiyar kudi na Opay.

Wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, inda ya ce ya yi amfani da kudin ne wajen yin caca da BetNaija.

Alkalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya yanke masa hukuncin daurin watanni uku bisa samunsa da laifin cin amana da kuma wata shida saboda sata, sannan ya umarce shi da ya mayar da kudaden da ya sata na N300,000.

source: tori news

from opera news

Views: 15

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *