Yadda wasu Agwagi suka yi sanadiyyar ƙonewar jirgin saman Amurka a sararin samaniya

Yadda wasu Agwagi suka yi sanadin ƙonewar jirgin saman Amurka a sararin samaniya

Wani jirgin kasar Amurka ya tashi amma ya gamu da tsaikon da ya sanya shi saukar gaggawa saboda kama wuta da ya yi.

An ruwaito cewa, agwagi ne suka jawo jirgin ya fara ci da wuta, lamarin da ya kai ga saukarsa na gaggauta a Ohio ba tare da shiri ba.

Ya zuwa yanzu, hukumar filin jirgin saman ta yi bayanin gaskiyar abin da ya faru, ya kuma bayyana musabbanin tashin wutar.

Ohio, Amurka – Wani jirgin kasar Amurka na Boeing 737 ya kama da wuta a tsakiyar sararin samariya kafin direbansa ya gaggauta saukar gaggawa a filin sauka da rashin jirage na Ohio.

Rahoto ya bayyana cewa, jirgin ya samu tsaiko ne samakon mamaye shi da wasu gungun agwagwi mai tashi suka yi, rahoton Punch.

Lamarin an ce ya faru ne jin kadan; akalla mintuna 40 bayan da jirgin ya tashi a ranar Lahadi 23 ga watan Afrilun 2020.

A cewar rahoton Mail Online, biyu daga cikin fasinjojin jirginl Marni Kallestad da Ryan Brink ne suka dauki bidiyon yadda injinsa ya kama da wuta.

Daga ina jirgin ya tashi?
Jirgin na American Airline da ya nufi Phoenix a birnin Arizona ya tashi ne daga filin jirgin sama na kasa da kasa na John Glen Columbus da misalin karfe 7:43 na safe, inda ya gaggauta sauka da misalin karfe 8:22 na safe, kamar yadda kafar FlightAware ta nuna.

Wani ganau na yadda jirgin ya smau tsaiko ya ce, jirgin ya gamu ne da wasu tarin agwagi masu tashi a lokacin da ya tashi, wanda hakan ya sanya tartsatsin wuta ya kama a injinsa nan take.

Sai dai, a wani rubutun gyara zance da aka yi a Twitter, hukumar filin jirgin ta ce, an samu matsaloli da ba a rasa ba, amma ba injin ne ya kama da wuta ba.

Views: 25

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *