Banji dadi da iyaye suka daina Auren dole ba—Jamila Ibrahim

Postin Din Da Jamila Tayi

Kamar yadda kuka sani shafukan sada zumunta na social media musamman Facebook sun shahara wajen kawo muhawara musamman yan mata sun shahara wajen yin posting na jawo hankali, Jamila Ibrahim ta ce nifa na gaji da soyayya ayi min Auren dole, inji Jamila Ibrahim (Home Of Solace)

Shahararriyar shugabar ƙungiyar nan ta kafar sada zumunta wato ‘HOME OF SOLACE’ Jamila Ibrahim ta bayyana cewar, sam bata ji daɗi ba da iyaye suka daina yin auren dole.

Ta ƙara da cewar; “Nifa na gaji da soyayya ayi min ta dolen, kullun kalmar bata wuce I love you.” Inji ta

Mutane da dama ne sukayi ta bayyana ra’ayoyinsu akan wannan batu nata, inda wasu suke cewar ta sauƙaƙa ta gani idan ba’a aureta ba, wasu matan kuma suka bayyana cewar suma sunyi na’am da wannan ra’ayi nata.

Kunji fa kuma ku bayyana ra’ayoyinku dangane da wannan batu menene ra’ayoyinku?

Views: 16

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *