Yadda Giwa ta saci buhun shinkafa a Thailand

Abin al’ajabi ba ya karewa a duniya rahotanni sun nuna cewa Giwa ta saci buhun shinkafa a dakin dafa abinci a kasar Tailand.

Rahotannin sun bayyana cewa, “Wata katuwar Giwa ta kunna kai cikin wani gida, inda kai tsaye ta tunkari dakin dafa abinci kuma ta sunkuci buhun shinkafa da kabewa da sauran kayan abinci”.

Lamarin dai ya ja hankalin al’umma wannan lamari dai ya faru a lardin Hua a kauyen Hin a gabashin kasar Thailand a ranar ashirin ga watan Yunin da muke ciki.

A bangare guda masu gidan ne dai suka kama wannan Giwa, kuma yanzu haka suna shirin gurfanar da ita a gaban Kuliya domin fuskantar hukunci.

Menene ra’ayoyinku?

Views: 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *