Ƴan bindiga suka kashe ɗalibar Jami’ar Bayero saboda iyayenta basu biya kuɗin fansa ba

/FSafdnaM83s

Masu satar mutane sun kashe daliba ta Jami’ar Bayero, Kano (BUK), mai suna Talatu Salihu, masu garkuwar sun bayyana cewa iyayenta ba su iya kawo kudin da suka buƙaci abasu ba don su sake ta.

/ekyZDZHK4Tk?si=QpBDM1fctHJqDJf3

Talatu Salihu, dalibar tana shekara ta ƙarshe a Jami’ar Bayero, Kano (BUK), masu satar mutane sun kashe ta da bayan da suka sace ta tare da yan uwanta a gidansu a Abuja, babban birnin Najeriya.

/ivBdNWGC1z8

Talatu daliba ce dake fannin Library and Information Science kuma an kashe ta bayan iyayenta ba su iya biya kudin da masu satar mutane suka buƙaci ba.

/bWUkNiaxXCw?si=PL5Tykzovqot7YWA

Abokai na kusa da Talatu a makaranta sun tabbatar da mutuwar ta ga SaharaReporters a ranar Laraba.

“An sace ta tare da yan uwansa biyu a Abuja kuma masu satar mutane suka buƙaci kudi fiye da miliyan 100 a matsayin kudin fansa wanda iyayenta suka gaza biya. 

“Sun kashe ta saboda iyayenta ba su iya biya kudin da suka buƙata ba,” Kawar Talatu ta sanarwa da SaharaReporters.

Ta ce masu satar mutane sun ci gaba da rike yan uwanta da akai garkuwa dasu wanda sukai barazanar cewa idan ba’a biyasu kudin da suka nema ba za su kashe su.

Views: 81

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *