A wata fira da sashin hausa na BBC Safara’u wacce ake yiwa laƙabi da Safara’u Kwana Casa’in ta bayyana cewa kashi 70% na ƴan mata masu amfani da wayar Android ko iPhone.
Suna ɗaukar hoton sassan jikinsu a waya.domin ganin yadda suke, saboda haka ba ita kaɗaice ke yi ba.
Safarau ta ƙara da cewa bata san yadda ka yi har faifan bidiyon tsiraicin ta ya fita ba ita dai kawai ta san cewa tana ajewa domin gani.
A wani labarin kuma da muka samu a gaggauce yanzu yanzu.
DA ƊUMI-ƊUMI: SSS sun kama kwamandan ISWAP da ke da hannu a harin bam kusa da fadar Ohinoyi
Hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, ta kama wani kwamandan ISWAP da ake zargin ya kai harin bam a kusa da fadar Ohinoyi na Ebiraland a Okene, jihar Kogi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Peter Afunanya, ya fitar, ya bayyana sunan wanda ya shirya harin, Abdulmumin Ibrahim Otaru, wanda aka fi sani da Abu Mikdad.
“Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) na sanar da jama’a cewa ta kama wanda ya shirya harin bama-bamai da ababen fashewa da suka faru a ranar 29 ga watan Disamba, 2022, kusa da fadar Ohinoyi na Ebiraland a Okene, Jihar Kogi a ziyarar da shugaban kasa ya kai domin kaddamar da wasu ayyuka.
“Hukumar ta kama Abdulmumin Ibrahim OTARU (aka Abu Mikdad) da daya daga cikin abokansa, Saidu SULEIMAN a ranar 3 ga Janairu, 2023. OTARU ya samu rauni daga harbin bindiga a kafarsa ta hagu yayin da yake kokarin tserewa. A yanzu haka yana karbar magani a wani asibiti.
” A yayin bincike, an tabbatar da cewa OTARU babban kwamandan Daesh ne na Lardin Yammacin Afirka (ISWAP) kuma ko dai shi ne ya kitsa harin, ko kuma yana da hannu a cikin wadannan munanan ayyuka,” in ji sanarwar.
Views: 11
