Za’a aiwatar da hukuncin kisan da Kotu ta yankewa sojan daya hallaka Sheikh Goni Aisami

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan



Bayan ya ƙare shure-shurensa, daga ƙarshe dai maras imanin nan da ya kashe Sheik Goni Aisami ya girbi abinda ya shuka.

A yau Babban Kotun Jihar Yobe da ke zama a Potiskum ta yanke wa wannan maci amana hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta kama shi da laifin kisa da fashi da makami. Shi kuma abokinsa, wanda ya je ya taimake shi bayan yayi kisan, ya samu daurin shekara 10 a gidan ɗankande.

Muna godiya ga gwamnatin Jihar Yobe a kan jajircewarta a kan wannan magana, kuma muna kira ga gwamnatin da ta gaggauta rataye wannan dabba da zarar ya gama afil ko kuma lokacin afil dinsa ya wuce. Shi kuma Mallam, muna ƙara roƙon Allah Ya lulluɓe shi da rahamarSa, Ya albarkaci bayansa.

Views: 8

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *