Ina neman mijin aure na hardace Alqur’ani kuma ina aiki a ƙasar Saudiyya—Zahra

Wata matashiya ta bada cigiyar mijin aure, matashiyar mai suna Zahra tacr tana aiki a kasar Saudiyya.

Hisbah a Katsina ta karyata zargin cin zarafin wata mata

Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta karyata rahoton da ke zargin jami’anta da dukan wata mata mai suna Hauwa’u Lawal.

Muhammad Shu’aibu, Mataimakin Kwamanda bangaren Ayyuka na hukumar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Lahadi a Katsina.

A wani faifen bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Hauwa’u Lawal ta zargi jami’an hukumar da dukan ta, wanda ya haddasa mata karaya a ƙafa da kuma raunuka da suka rage mata jin kunne.

Matar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da ta ziyarci ɗan uwanta wanda ke tsare a hannun hukumar.

A martani na gaggawa, Malam Shu’aibu ya tabbatar da kama wani mutum wanda shi ne ɗan uwan matar.

Ya ce an kama mutumin ne bisa zargin tsoma baki cikin aikin jami’an hukumar yayin da suke bakin aiki, da kuma nuna kansa a matsayin soja.

“An hana ta shiga ne saboda irin yadda ta sanya kaya marasa kamun kai, amma ta dage da son shiga har ta kai ga yunkurin dukan ɗaya daga cikin jami’an.”

Views: 7965

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *