Yadda ake gane maccen da bata da kwaɗayin abin Duniya

Yadda zaka fahimci macen da bata da kwadayin abin duniya……

1⃣.zaka jima tare da ita amma bazata taba rokon ka kayi mata abu ba,ba zata nuna maka tana son abin hannun ka ba ita kai ne take so.

2⃣.Ba zata baka labarin kyalkalin abin duniya ba,wato ko kaya ne ko wani abu haka bazata iya gaya maka ba.

3⃣.Ba zata dinga maka labarin kawayen ta sun rike manyan wayoyi ba ko suna saka sutura mai tsada ba.

4⃣.Ba zata taba nuna maka dole sai kayi mata abu ba koda ace tana son abin nan zata yi Alkunyar gaya maka.

5⃣.Ba zata taba daukar rayuwar duniya da zafi ba,komai zaka same ta tana binsa a hankali, kullum ba zaka ji tana nuna maka iko ba.
Tana daukar rayuwar ta a hankali kyalkalin duniya bai dame ta ba.

Irin wannan macen idan ka same ta kayi kokarin rike ta da kyau,kayi kokarin ganin ka aure ta domin macen arziki tushen zuri’a mai kyau ne.

Kayi kokarin kyautata mata daidai karfin ka,zaka sha mamakin irin farin cikin da zata dinga nuna maka komai kankantar abu kayi mata.

©️ Nusaiba Tasiu Abdulrahim

Views: 7830

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *