Kotu ta wanke mutumin daya shafe shekaru 48 a gidan yari bisa zargin kisan kai a Amurka

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Mai shari’a a Oklahoma ta wanke wani mutum da ya shafe kusan rabin ƙarni a gidan yari saboda kisan kan da aka yi a 1974, hukunci mafi tsawo da aka taɓa yankewa a Amurka.

An saki Glynn Simmons mai shekara 70 cikin watan Yuli lokacin da wani alƙali ya ba da umarnin a sake shari’a.

Sai dai wani lauyan gudunar ya ce babu isassun hujjoji da za su buƙaci hakan.

Mai shari’a ta gundumar Oklahoma,Amy Palumbo ta wanke Mr Simmons daga laifin.

“Wannan kotun ta samu gwamsasshiyar hujjar cewa ba Mr Simmons bane ya aikata laifin da ya sa aka same shi da laifi har aka yanke masa hukunci aka kuma kulle shi,” kamar yadda ta faɗa a hukuncin da ta yanke.

“Wannan darasi ne na juriya da jajircewa,” in ji Mr Simmons bayan hukuncin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito. “Kar ku yadda wani ya ce hakan ba za ta taɓa faruwa ba, saboda lalle zai iya faruwa.”

Mr Simmons ya shafe shekara 48 da wata ɗaya da kwana 18 a gidan yari saboda kisan Carolyn Sue Rogers lokacin wani fashi a kantin sayar da barasa a wata unguwa da ke Oklahoma. Hakan ya sa ya zama fursunan da aka wanke wanda ya fi daɗewa a gidan yari, a cewar hukumar da tattara bayanan mutanen da aka wanke daga laifi.

Mr Simmons yana shekara 22 lokacin da aka same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin kisa a 1975.

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *