Shugaban Nijar ya yiwa Faransa kaca-kaca

Shugaban Nijar Da Na Faransa

Masana harakokin siyasa a kasar Jamhuriyar Nijer, sun fara bayya ra’ayoyinsu dangane da kalaman da shugaban kasar Muhammad Bazoum ya furta a kasar Faransa lokacin da ya kai ziyara ga shugaba Emmanuel Macron na kasar ta Faransa inda yace.

Shugaba Mohamed Bazoum ya bayyana cewa bamu da bukatar sojojin ku na Faransa a kasar mu idan kuna son ku taimake mu dagaske, to ku bamu tallafin tsabar kudaden da zamu sayi makamai ko kuma ku bamu makaman sannan ku taimaka mana da fasahohin zamani.

“Dole ne mu dogara da sojojinmu a wannan yaki da ta’addanci, babu wani sojan Faransa ko na wani waje da zai iya yi mana wannan yakin ta hanyar da ta dace.”

“Abinda kawai muke bukata daga abokanmu shine hanyoyin kudi da fasaha, amma ba sojojin kasashen waje 1000 ko 10,000 ba”

Views: 9

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *