
Me yasa wasu ma’auratan ke sakin hotunan iyalansu a kafafen sada zumunta na zamani duk kuwa da sanin cewa hakan babbar illa ce a garesu nan gaba musamman idan suka fara tara iyali?
Wannan dai tambaya ko kuma in ce tambayoyi an dade ana yinsu amma har kawo yanzu babu abinda ya sauya duk kuwa da cewa Malamai na yin wa’azi akan hakan inda suke cewa sam bai dace ba.
Wani bincike ya nuna cewa wannan lamari ya kara yaduwa da kashi biyar a wannan shekarar ta 2021 idan aka kwa tanta da shekar 2020 da ta gabata.
Wasu dsi na ganin cewa ma’auratan na yin hakanne don kawai su nunawa duniya cewa suna jin dadin zamansu na aure saboda idan babu soyayya da zaman lafiya hakan ba mai yiwuwa bane.
Amma ku menene ra’ayoyinku?
Views: 376
