
A wata sanarwa a yammacin yau shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ƙasar “ta yi sa’a” da har yanzu ba ta rabe ba duk da irin ƙalubalen da aka fuskanta da ka iya wargaza ta.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake karɓar rahoton Kwamitin Taron Tsaro na Ƙasa da aka yi ranar 26 ga watan Mayun 2021 daga Majalisar Wakilai.
Wasu Yan majalisa ne suka gabatar wa da shugaban rahoton ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ranar Talata.
Inda ya ce Mu Najeriya ƙasa ce mai sa’a kuma ya kamata mu yi wa kanmu murna, duk da barazanar da muka fuskanta da ka iya raba kanmu,” in ji shugaban cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar.
Shugaba Buhari ya shawarci shugabanni da su girmama al’umma na ƙasa da na sama ta yadda “[mutanen] za su lazumta wa kansu mayar da alherin da aka yi musu”.
Kuma ya ci gaba da cewa girmamawa ga mutane ita ce “a ƙyale su su zaɓi wanda suke so a matsayin shugbansu ba tare da nuna bambancin jam’iyya ko addini ba”
©BBC Hausa
Views: 7
