An maka shugaban Najeriya kara a Kotun ICC

Shugaba Muhammadu Buhari

Wasu gungun kungiyar Yarabawa ta Ilana Omo Oodua a Najeriya, da wasu kungiyoyi 49 sun maka shugaba Muhammadu Buhari gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC inda suka gabartar da wasu takardun korafi mai dauke da shafuka 27.

Rahotanni sun ce shugabanni da yawa na Kungiyoyin Kafa kasar Yarabawa ciki har da Farfesa Banji Akintoye, da Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ne suka rattaba hannu a takardun korafin wanda jaridun Najeriya suka tabbatar da shi.

Kuma rahotanni daga kasar sun lura da cewa an gabatar da korafin gaban kotun ta ICC ne a madadin shugabannin wasu kungiyoyin Yarabawa ta hannun wani lauyan kasa-da-kasa mai suna Aderemilekun Omojola.

Bugu da kari a cikin takardar karar, an zargi wasu shugabannin Najeriya da aikata kisan kare dangi, cin zarafin bil’adama akan al’ummar ta Yarbawa da ke jihohin Ekiti da Oyo da Osun da Ondo da Ogun da kuma garin Okun da ke jihar Kogi da Kwara na kasar.

©RFI Hausa

Views: 24

2 thoughts on “An maka shugaban Najeriya kara a Kotun ICC

  1. Al -Umarda tasan kanta kenan amma Bahaushe in zaka rataye dan uwansa shi ne zai rikema igiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *