
A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani gagarumin aikin layin dogo a jihar Kano, tare da wasu muhimman manyan ayyuka da mai girma gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya gudanar a cikin da wajen birnin jihar ta Kano.
A yayin da yake jawabi shugaba Buhari ya yabawa gwamna Ganduje tare da cewa wadannan ayyuka sun zama gagarumin zakaran gwajin dafi ga gwamnonin da suka gabata dama wadanda za su zo nan gaba, shugaban ya ce, “tarihi bai nuna wani gwamna da ya taba yin gagaruman ayyuka kamar na gwamna Ganduje da ya gudanar a halin yanzu yafi ko wane gwamna aiki a tarihin jihar ta Kano,” in ji shugaban.
Wannan kalamai na shugaban dai sun jawo muhawara a fadin jihar ta Kano, inda wasu ke ganin shugaban yana nufin har gwamnatin Kwankwaso da ta gabata bata yi ayyuka kamar na wannan gwamnatin ba kenan? Wannan ita ce tambayar da wasu ke yi.
Ga kadan daga cikin hotunan ayyukan da Gandujen ya gudanar

Hoto Na Biyu

Hoto Na Ukku

Hoto Na Hudu
Hoto Na Biyar

Hoto Na Shidda

Views: 25

