“Yan bindiga sun sako mutanen da suka kama a matsayin barka da Sallah”

Hoto daga sunnews

Jaridar Katsina Post ta bada rahotin cewa “Yan bindiga sun sako mutum 4 daga daji matsayin barka da Sallah a Katsina”

Daga misbahu batsari

A ranar Juma’a 23-07-2021 aka sako wasu daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka dauka a Batsari.

In ba’a manta ba, watanni biyu da doriya da suka gabata ‘yan bindiga masu satar shanu da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, suka dirar ma wasu unguwannin Batsari, inda suka kashe mutum daya, sannan suka sace mutane 28 da tarin dabbobi.

A ranar Juma’a Allah yayi fitowar wasu daga cikinsu.

Zantawar Katsina Post da mutanen da aka sako sun bayyana mata irin bakar azabar da suka sha ta yunwa da sauran kuncin rayuwa a zaman su dajin, inda har wani yaron goye ya rasa ransa.

Rahotanni sun ce an biya zunzurutun kudi kudi har naira miliyan biyu da rabi N2.5m da zimmar karbo matar Umar Tukur mai suna Hussaina da jinjirinta Al-ameen, sai suka karo masu da mutum hudu, sukace ga barka da sallah nan kamar yadda suka labarta mana.

Ga jerin sunayen mutanen da aka sako:

  1. Hussaina Umar.
  2. Al-ameen Umar.
  3. Marwanatu Bello.
  4. Zainab Bello.

Kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Views: 10

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *