“Yau za’a gurfanar da Abduljabbar gaban Kotu”

GDAGA SHAFIN ASHABULKAHFI GAME DA ZAMAN SHARI’AR DA ZA’A FARA TSAKANIN DR SHEIKH ABDULJABBAR KABARA (H) DA GWMANTIN KANO.

A ranar Laraba 28/07/2021 ne za’a fara zaman sauraren shari’ar kamar yadda aja sanar.

Don haka muna amfani da wannan damar domin jan hankalin ‘Yan Makaranta, Duk Wanda Ya Sami Damar Zuwa Kotun

Ya Kasance Cikin Da’a Da Biyayya Ga Doka Da Oder Kamar Yadda Aka Sammu.

Domin Mun sami rahoton masu kulla mana makirci sunyi kakkarfan shiri sun debi mutane da nufin suyi basaja su shiga cikinmu domin tada fitina da sunanmu.

A sahun farko muna jan hankalin wadanda zasu sami halarta daga Yan Makaranta, cewa kada su rudu ko su sauka daga layin nan da aka sansu na da’a da bin doka da oda.

Na biyu muna kira ga hukuma data sa ido kan wadannan bata gari da ake nufin shigo dasu don su tada husuma, kuma muna shaidawa duniya barrantar mu da makarantar Mujamma’u Ashabil Kahfi Warraqeem Nigeria Baki daya da Jagoranmu(H) daga irin wannan aiki.

Ana kira ga yan uwa dasu lazimci addu’a kamar yadda aka saba, da rokon Allah yayi riko da hannun mahukunta izuwa adalchi.

Tuesday, 27th, July, 2021
Mujamma’u Ashabil Kahfi Warraqeem

Views: 22

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *