LABARI DA ƊUMI-ƊUMI: Jami’an FBI sun sauka Najeriya domin kama Abba Kyari

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Jami’an Tsaron FBI Na Ƙasar Amurka Sun Zo Najeriya Suna Neman A Basu Abba Kyari Su Tafi Da Shi

Rahotanni daga Abuja na cewa a ranar Alhamis, jami’an tsaron FBI na ƙasar Amurka sun gana da shugaban ƴan sandan Najeriya dan neman a basu Abba Kyari su tafi da shi.

Rahoton ya bayyana cewar jami’an FBI 4 ne suka zo Najeriya inda suke neman a basu Abba Kyari dan su je su tuhumeshi a ƙasarsu.

Kazalika kuma majiyar ta ƙara da cewa jami’an na FBI sun sake komawa a yau Juma’a inda suke neman sai fa an basu Abba Kyarin.

Views: 23

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *