FBI ta wallafa tattaunawar WhatsApp tsakanin Abba Kyari da Hushpuppi

Hoto Daga Google

A yammacin jiya ne hukumar dake gudanar da binciken manyan laifuka ta kasar Amurka Federal Breuer Investigation wato (FBI) a takaice ta saki tattaunawar da aka yi tsakanin dan damfarar nan Hushpuppi da jami’in dan sanda Abba Kyari wanda wasu daga cikin manyan jaridun Najeriya irin su Thisday suka wallafa a shafukansu, zaku iya karanta cikakkiyar tattaunawar idan kuka ziyarci jaridar Thisday.

Sai dai tuni wasu daga cikin magoya bayan Abba Kyarin suka dukufa wajen kare shi da nuna masa goyon baya a shafukansu na sada zumunta ga kadan daga cikinsu.

Datti Assafi:

BA YADDA SUKA IYA DA IKON ALLAH

Duk lokacin da na ziyarci lahiran kidnappers a Abuja wato babban sansanin rundinar Intelligence Response Team (IRT) na hadu da Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari gadanga kusar yaki, ya kan ce dani Datti Assalafiy ikon Allah, a raina sai nace Sarkin Yaki ai kaine ikon Allah

Duk jami’an tsaron Nigeria babu wanda ‘yan ta’adda da maciya amanar tsaron Nigeria suke jin haushinsa kamar DCP Abba Kyari, imba don ikon Allah ba; babu yadda za’ai mutum ya tara tulin makiya ‘yan ta’adda basu kai shi kasa ba, amma har yanzu DCP Abba Kyari yana tsaye da kafafunsa, saboda gaskiyarsa, kuma Allah Yana tare dashi, don haka duk wanda yace zai ja da ikon Allah sai ya fadi kasa

A birnin Lagos an kai wani mizani da manyan barayi suna neman cin karfin jami’an tsaro, amma lokacin da aka nada DCP Abba Kyari kwamandan SARS sai da aka wayi duk wani gang leader na barayi a jihar Lagos DCP Abba Kyari ya kamasu, wasu sun tafi garin da ba’a dawowa

Lokacin da aka nada DCP Abba Kyari kwamandan IRT, duniya ta shaida da irin namjin kokarin da yayi wajen kama manyan shugabannin masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda a sassan Kasarnan, Abba Kyari yana kwana aiki a cikin ofis dinsa bai runtsa ido ba, idonsa na kan na’urori yana neman bahasi da maboyar masu garkuwa da mutane daga tauraron ‘dan-Adam, gari ya waye ya jagoranci mutanensa zuwa maboyarsu a fafata

Abba Kyari bai tsaya anan ba, ya yaki Boko Haram, ya kama shugaban kungiyar Ansaru reshen Boko Haram, ya kama manyan Kwamandandojin yakin Boko Haram da suka gagara kamuwa, Abba Kyari shine ya kama ‘yan Boko Haram din da sukayi garkuwa da ‘yan matan Chibok, ya kama daruruwan ‘yan Boko Haram wanda ba zasu kirgu ba, duk da ba bangaren aikinsa bane, amma a haka ya taimaka

Kwanan nan tsagerun IPOB/ESN mutanen Nnamdi Kanu suka dauki makami suka taso da zummar zasu durkusar da Gwamnatin Nigeria tare da haddasa fitina da yaki, DCP Abba Kyari shi kadai ya kama manyan Kwamandandojin yakin IPOB, ya karya alkadarinsu, ya hana musu cikar burinsu, ya aika wasun su zuwa garin da ba’a dawo wa domin su ansa laifukan da suka aikata a gurin Ubangiji

Suwaye suke daukar nauyin IPOB? ku tuna cewa babban asusun ajiyar kudin banki na kungiyar IPOB yana Kasar Amurka, wato kai tsaye Amurka da Burtaniya suna tare da IPOB suna karfafansu suna basu mafaka, kuna tsammanin ba zasu iya bada gudunmawa wajen durkusar da Abba Kyari ba saboda ya tsaya musu a wuya?

Jama’a ku tuna cewa, kwana biyu da suka wuce, ‘yan majalisun Kasar Amurka suka kada kuri’ah akan batun sayarwa Gwamnatin Nigeria makamai, mafi rinjayen ‘yan majalisun Amurka suka kada kuri’ah akan cewa kada a sayarwa Kasarmu Nigeria jiragen yaki, a dalilin wai Gwamnatin Nigeria tana take hakkin bil’adama, alhali duk duniya babu Kasar da ta kai Amurka taka hakkin bil’adama, duniya ta ga abinda Amurka tayi a Afghanistan da Iraqi da Libya

Abinda baku sani ba shine Amurka da kasashe ire-irenta basa kaunar Nigeria ta shawo kan matsaloli na tsaron ta, suna karfafan mutanen da suke yunkurin haddasa yaki a Nigeria ta karkashin kasa, ku tuna da gargadin da Amurka da Burtaniya suka yiwa Nigeria lokacin da masu zanga-zangar ENDSARS suka tashi kone Nigeria da wuta da fasa shagunan mutane

Abinda DCP Abba Kyari kadai ya yiwa IPOB ya kai su yakeshi, sun fito ta wannan sigar a yanzu da nufin yakarsa, ina mai tabbatar muku da ikon Allah ba zasu kai ga nasara ba

Yaa Allah Ka tsare mana rayuwa da mutuncin Sarkin Yaki DCP Abba Kyari, Allah Ka daukaka darajarsa, Ka kunyatar da makiyansa makiya zaman lafiyar Nigeria Amin.

Barr Hamza N. Dantani.

MAKIYA SUN SAKE BIJIRO DA SABON SHARRI

Sanannen abune a rayuwa duk lokacin da dakarun tsaro suka fito suna yaki da miyagun mutane masu aikata munanan laifuka to jami’an tsaron sai sun fuskanci hari daga masu aikata laifukan

DCP Abba Kyari ya sadaukar da lokacinsa da basiransa da jin dadinsa na tsawon shekaru 20 yana fada da miyagun mutane domin ya kare Kasarmu Nigeria, ya kasance babban abin tsoro ga wadanda suke aikata miyagun laifuka a cikin gida Nigeria da waje, nasaran da ya samu a yaki da ‘yan ta’adda ba zai lissafu ba

Don haka ba abin mamaki bane don wakilan ‘yan ta’adda sun hada baki domin su bata masa suna ko don su durkusar dashi a kowani lokaci

Ta ya za’a ce mutumin da ya taimaka wajen kama manyan ‘yan ta’adda da masu aikata miyagun laifuka a Kasarnan zai hada kai da wani ‘dan damfara ya karbi cin hanci domin ya boye wanda ake zargi daga fuskantar shari’ah?

Gaskiya ne DCP Abba Kyari ‘dan-Adam ne kamar kowa zai iya yin kuskure, amma ba yadda za’ayi ya hada kai da miyagun mutanen da yake yaka domin cin amanar kasa

Anan nake kira ga ‘yan Nigeria mu hadu mu tashi tsaye mu kare mutuncin jaruman mutane irin DCP Abba Kyari daga sharrin mutanen da basa nufin Kasarmu da alheri, DCP Abba Kyari zai cigaba da kasancewa abin bakin ciki da bala’i ga ‘yan ta’adda a Nigeria

Sannan zamu cigaba da bash gudunmawa da karfin gwiwa a cikin dukkan lamarinsa, munyi imani da Allah cewa rundinar adalci da gaskiya zata cigaba da samun nasara akan rundinar miyagun mutane, shaidanu da marassa adalci

Views: 10

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *