Twitter ya ce ya hakura da kasuwanci a Najeriya

Kamfanin sadarwa na Twitter ya bayyana cewa dokokin da gwamnatin Najeriya ta sanya masa sun yi tsauri dayawa kuma wasu daga cikinsu ma sun sabawa kundin tsarin dokomin kamfanunsa, saboda haka.

Ya nemi gwamnatin da ta sake duba hukunce hukuncen da ta gindaya masa dare da wasu ka’idoji masu tsaurin gaske, domin kuwa ba shi kadai ne kamfanin sadarwar da ke gudanar da kasuwanci a kasar ba.

Idan kuma ba haka ba zai hakura da gudanar da kasuwancinsa a kasar har sai an samu gagarumin sauyin gudanar da tsarin mulki a kasar kafin komai ya dai daita.

A cewar sakataren gudanarwar kamfanin kamar yadda jaridan Post ta ruwaito a ranar Juma’a, yau kimanin watanni ukku kenan da gwamnatin kasar ta dakatar da shafin a fadin kasar bisa zarginsa da taimakawa masu tada kayar baya a ciki da wajen kasar.

Wata kididdiga dai ta ce kimanin naira miliyan dubu daya da dari biyar ne yan kasar suka yi asara tun lokacin da aka dakatar da shafin.

Menene ra’ayoyinku.

Views: 26

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *