
Sabbin yan Boko Haram 100 sun sake mika wuya ga gwamnatin Najeriya
Wasu sabbin yan ta’addan Boko Haram sama da 100 sun mika wuya ga Sojoji a Borno
Wasu kwamandoji ne suka jagoranci yan ta’addan zuwa wajen Sojoji a Gwoza
Har yanzu gwamnatin Najeriya na nazari kan yadda zata yi da wadannan yan ta’adda masu mika wuya,
Gwoza LGA, jihar Borno – Yan ta’addan Boko Haram sama da mutum 100 tare da iyalansu sun mika wuya ga hukumar Sojojin Najeriya a jihar Borno.
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan abu ya auku ne a garin Gwoza, karamar hukumar Gwoza ta jihar.
An tattaro cewa wani kwamanda ne daga cikin kwamandojinsu ya jagoranci mutum 120 zuwa wajen Sojojin.
Wata majiya mai karfi ta tabbatar da cewa wadannan yan Boko Haram sun mika wuya ne tare da iyalansu ga rundunar 26 task force brigade dake Gwoza.
Shin yaya kuke ganin wannan tuban??
Views: 10
