Najeriya za ta ƙaddamar da sabbin kuɗaɗenta na Intanet wato e₦aira

eNaira: Za A Kaddamar Da Sabuwar Kudin Internet Na Najeriya Ranar 25 Ga Watan October

Daga: Mujahid Lawal S Jumare

Babban bankin Najeriya, CBN ta fitar da sanarwan an gama tsara cewar Shugaban kasa Muhammad Buhari, a ranar 25 ga wannan watan ta October zai kaddamar da sabuwar kudin Najeriya wanda za a iya amfani da shi ne kawai a yanar gizo-gizo wanda ake masa lakabi sa eNaira.

Babban bankin ta bayyana cewa, za a fitar da sabuwar kudin ne bayan dogon bincike da nazari da bankin Najeriya, CBN ta yi na tsawon shekaru domin a saukaka hanyar yin hada-hadan kudi da cinikayya a lungu da sakon kasarnan.

CBN, ta jaddada cewa za a kaddamar da sabuwar kudin a ranar litini mai zuwa 25 ga watan October a Abuja.

Idan dai ba ku manta ba, a makon da ta gabata ne Babban bankin Najeriya ta fitar da sanarwan cewa za a kaddamar da kudin yanar gizo-gizon ne a yayin da ake bikin murnan samun yanci amma, wasu uzururruka ya hana kaddamar da kudin.

A gefe daya kuma, ma su hada-hadan kudi na internet da ke kan fasahar block chain su na ta kushe sabuwar kudin da za a kaddamar. A cewarsu, ai ba shi da wani banbanci da kudin da ake amfani da shi a bankuna.

Binciken jaridarmu ta Manuniya ta gano cewa, ma su hada-hadan kudi internet, na Crypto, har yanzu su na cike da jin haushin hana bankuna shiga harkokin Crypto da babbar bankin Najeriya, CBN ta yi a watannin baya duk da cewa hakan bai hana su ci gaba da gudanar da cinikayyarsu ba ta hanyar wani tsari da a ke kira P2P musamman a babbar kasuwar Binance.

Views: 9

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *