Yadda al’umma ke gudun hijira daga garin shimfida a ƙaramar hukumar jibia dake jihar katsina

ABIN TASHIN HANKALI | Yadda Al’umma Suke Gudun Hijira Daga Garin Shimfida A Ƙaramar Hukumar Jibia Dake Jihar Katsina.

Daga Comr Nura Siniya.

A ranar Alhamis 10/03/2022 ne wasu ‘yan bindiga suka shiga garin shinfiɗa inda sukai ta harbe harbe har suka kashe mutun 7 tsakanin maza da mata tare da yin garkuwa da mutun goma sha ɗaya wanda har yanzu ba amo ba labarinsu.

A Hakan ya faru ne a dilillin janye Jami’an tsaron da aka yi a yankin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan bindigar sun kwashe abincin garin da kayayyakin sawa na mutane kuma har yanzu Ba muji Wani Matakin Da Aka Ɗauka Ba Akan Janye Jami’an Tsaron Dake Ƙauyen Shimfida Ƙaramar Hukumar Jibia Jihar Katsina Najeriya.

A yanzu haka mutanen da suka yi gudun Hijira daga garin shinfiɗa suna nan jibge a Makarantun firamare a cikin garin Jibia.

Ya kamata Gwamnati da jami’an da sauran masu ruwa da tsaki su gaggauta karkato da hankalinsu wajen kare rayukan al’ummar garin shinfiɗa da sauran garuruwan dake fama da matsalar tsaro a jihar Katsina.

Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan masifa.

Views: 9

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *