Jagoran Shi’a shaikh Zakzaky ya zaɓi ɗan takarar da zai marawa baya shi da mabiyansa

Jagoran Ƴan Shi’a Sheikh Ibrahim Elzakzaky

Wasu rahotanni da ke yawo a kafafen watsa labarai na zamani wato Social Media na cewa jagoran ƙungiyar Islamic Movement of Nigeria, sheikh Malam Ibrahim Elzakzaky ya bayyana cewa.

Magoya bayansa su kaɗa ƙuri’ar su ga ɗan takarar shugaban ƙasa, na jami’ar New Nigeria People Party (NNPP) Eng Dr Rabi’u Musa Kwankwaso a zaɓen 2023 mai zuwa.

Sai dai bisa bincike da sashin Hausa ya gudanar kan wannan batu, ya tabbatar da cewa shehun malamin bai ware wani ɗan takara ɗaya tilo yace magoya bayansa su zaɓa ba, kawai dai ya yi kira ga al’ummar Najeriya ba magoya bayansa kaɗai ba.

Da su zaɓi can canta kuma aci gaba da addu’ar samun shugaba nagari.

Views: 13

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *