Za’a kai shi Kotu a karon farko Aisha Buhari ta yi magana game da batun kama Aminu Muhammad

Hoton Aisha Buhari

Wasu rahotanni na nuni da cewa yau za’a tasa ƙeyar ɗalibin nan dabya yi rubutu a kan uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari Kotu domin amsa tuhuma.

Wanda wasu ke alaƙanta hakan da cewa nayi magana akan shurun da tayi domin kuwa idan wannan rahoton ya tabbata gaskiya to babu shakka ta nuna cewa dagaske ita tasa aka kama shi.

kamar yadda shafin Datti Assalafy ya ruwaito.

ABIN KUNYA

Da gaske fa matar nan ita ta sa aka kama yaron nan

Yau zasu kaishi Kotu a Abuja

Tayi deactivating Twitter account dinta don an demata da tagging

Nace ba, idan kin ga dama ki sa a kashe shi, karshen abinda zaki iya yi kenan na zalunci

Ke kuma kar ki mutu idan kin isa, ko kuma ki tabbata akan mulki idan kin sani

Abin kunya kawai

Aisha Buhari dai na cigaba da shan suka game da wannan al’amari daga bakunan manya da ƙananan ƴan Najeriya.

Views: 12

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *