Wayar ₦1,200,000 ƙirar Samsung da Kabir Gombe ke riƙewa ta jawo ce-ce-ku-ce

Jama’a nata cece kuce a shafukan sada Zumunta inda aketa yada hotunan fitaccen malamin Addinin Musulunci watau Sheik Kabiru haruna gombe rike da wayar samsung mai tsada.

Wacce aka ƙiyasta cewa ta kai Kimanin kudin Najeriya naira Miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin (1,250,000) a hannun malamin.

A yayayin gudanar da wani taro ne dai aka ga wayar a hannun shehin malamin addinin Islamar wanda ke riƙe da muƙamin sakataren kungiyar Izala na ƙasa.

Sai dai wasu na ganin cewa wannan ba wani abun tayar da jijiyoyin wuyane ba da za’a yi cece kuce a kansa.

Views: 8

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *