Wata budurwa ta nemi hallaka saurayinta ta hanyar amfani da guba, budurwar wacce ba’a bayyana sunanta ba a cikin bidiyon wanda yayi yawo a kafafen sadarwar internet.
An ganta zaune tare da saurayin nata suka ƙoƙarin shan lemu kwatsam sai ga manajan Hotel ɗin ya zo kansu ya faɗawa saurayin cewa kar kasha wannan lemun, inda faɗar hakan ya ba shi mamaki yace me ya faru?
Sai manajan Hotel ɗin yace masa an sanya guba a cikin wannan lemun inda yayi ƙoƙarin musanta masa, sai yace “Ka nemi wannan budurwar taka ta fara shan lemun kafin ka sha” sai taƙi amincewa ta sha lemun.
Sai yace ka biyo ni muje Office ɗina suna zuwa ya kunna masa hoton bidiyon da na’urar CCTV Camera ta ɗauka a dai dai lokacin da take sanya gubar.
Allah shi kyauta.
Views: 16
