Sana’ar talla tana da illoli masu ɗunbun yawa ga rayuwar mata musamman wanda sun munzalin yin aure.
Kamar yadda wata ƙididdiga ta nuna ajwai kinanin mata da ƴan miliyan 20 dake gararamba a kan titunan Najeriya suna gudanar da tallaci tallace iri daban da ban ga kaɗan daga cikinsu.
A mafi akasin garuruwan jihohin Arewacin Najeria, yana wuya kayi tafiyan minti guda baka ga ƴan mata suna talla ba.
Talla a bakin kasuwa ko makaranta, tasha ko masana’anta, wureren leburori ko kan titi, gidajen kallon kwallo ko sinima, filin kwallo ko gidajen damben gargajiya.
Babban abunda zai baka mamaki shine, yawancin abubuwan da suke sayarwa basa wuce abun Naira dubu daya ko dubu biyar, amma yarinya zata bar gidan iyayenta tun da safe har zuwa dare da sunan talla.