Ƴar NYSC ce ta haifi jaririn farko a 2023 a Ebonyi

Bautar ƙasa ko kuma yiwa ƙasa hidima wani aikin sa kai ne da ɗalibai ke yi a duk lokacin da suka kammala karatun digiri a jami’a.

Ƴar NYSC ce ta haifi jaririn farko a 2023 a Ebonyi

Uwargidan gwamnan Ebonyi, Racheal Umahi, ta tarbi jaririn farko da aka haifa a wannan shekara da misalin karfe 12.52 na safe a asibitin koyarwa na tarayya na Alex-Ekwueme, Abakaliki.

Jaririyar, mai nauyin kilogiram 3 a lokacin haihuwa, ma’aikaciyar kungiyar masu yi wa kasa hidima ta kasa, Chidimma Attah-Favour ce ta haifo ta a Ebonyi, amma ‘yar asalin garin Nsukka ta jihar Enugu ce.

Da take jawabi yayin ziyarar da ta kai ga jaririyar ta farko da aka haifa ta hanyar yi mata aiki, Umahi ta yi addu’a tare da gode wa Allah da ya ba su lafiya.

Ta yaba wa mahukuntan asibitin bisa jajircewa da kulawar da suka bayar na ganin an samu haihuwar lafiya.

Ta kuma bukaci iyaye da su yi renon jaririya4 yadda ya kamata domin kyautata rayuwar iyali da kuma al’umma.

Views: 9

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *