Nifa a halin yanzu da ka bani kyautar Naira Miliyan 5 gara ka aureni—Hauwa’u Abdullahi

Daga dandalin Twitter.

Kamar dai yadda kuka sani ƴan mata da samari na baje kolinsu a shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media.

Inda wasu ke amfani da kafafen na sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram, da dai sauransu wajen gudanar da harakokin da suka shafi kasuwanci.

Wasu kuma ke yin rubuce-rubuce da nufin jan hankalin mabiyansu wato followers, ta yadda za kuga ƴan mata da samari na yin abubuwan da zasu ɗauki hankulan abokansu na sada zumunta.

Wata budurwa mai suna Hauwa’u Abdullahi mai laƙabin Jiddarh a shafinta na Twitter ta bayyana wa Duniya cewa ita fa a halin da ake ciki yanzu da bata kyautar Naira miliyan biyar ƙwara a aureta kamar yadda zaku ga hoton Screenshot ɗin rubutunta daga ƙasa.

Ga ra’ayoyin wasu daga cikin mabiyanta.

A wani labarin kuma a fagen wasanni.

Ronaldo ya yi suɓutar-baki a Saudiyya

Shahararren ɗan ƙwallon ƙafar duniya Cristiano Ronaldo ya yi tuntuɓen harshe a lokacin da ake gabatar da shi ga sabuwar ƙungiyar da ya koma ta Al Nassr ranar Talata,

Ronaldo ya yi suɓul-da-baka a gaban magoya bayan ƙungiyar inda ya ce ‘South Afirka’ a maimakon ‘Saudi Arabiya’.

Ɗan wasan ya koma Al Nassr ranar Juma’a bayan da ya raba-gari da tsohuwar ƙungiyarsa Manchester United.

Ronaldo ya ce: “Wasan ƙwallon ƙafa wani abu ne na daban, dan haka zuwana ‘South Afrika’ ba shi ne ke nuna cewa ta-ƙare min ba”

”Wannan shi ne dalilin da ya sa nake son samun sauyi, haƙiƙa ban damu da abin da mutane ke cewa ba”, kamar yadda Ronaldo ya bayyana wa manema labarai a lokacin da aka gabatar da shi a birnin Riyadh.

Ya ƙara da cewa: “Na samu komai, na yi wasa a manyan ƙungiyoyi a Turai, a yanzu kuma lokacin buɗe sabon babi ne a Asiya”.

Bayan taron manema labaran, ɗan wasan ya sanya sabuwar rigar wasansa ta ƙungiyar a filin wasan a gaban dubban magoya bayanta.

Views: 21

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *