Ƴan Najeriya da dama na tururuwa zuwa bankuna don kai tsofaffin kuɗaɗen su a musanya musu da sabbi inda wasu kuma ke ƙoƙarin cire nasu yayin da wasu ke gudanar da sallar su a cikin bankunan.
A wani labarin kuma.
Rundunar ƴansandan Najeriya ta shawarci ‘yan Najeriya da su daina ɓatawa jami’an tsaro, musamman ƴan sanda suna a wajen matasa masu tasowa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ne ya ba da shawarar a jiya Lahadi a cikin wata sanarwa, yayin da ya ke martani kan wani faifan bidiyo da ya yadu, inda a ka nuno wani mutum ya ki amincewa da zabin ‘yarsa na yin aikin ɗansanda.
Shahararren dan wasan Nollywood na Najeriys da slsna cikin wani faifan bidiyo, an ga yadda yake baiwa yarinyarsa shawarar kada ta zama ‘yar sanda.
Jarumin ya shaida wa yaron a cikin faifan bidiyon cewa duk da cewa bai taba kyamar ‘yansanda ba, amma ya tsani irin hadarin da suke fuskanta da kuma rashin biyansu albashi.
Ya shawarci ‘yarsa da ta zabi zama maitukin jirgi, injiniya, likita, ko lauya, da dai sauran sana’o’i.
Kakakin Rundunar, ya yi gargadin cewa hakan na iya haifar da kyama ga cibiyoyin halal a zukatansu yayin da suke girma.
Views: 28
