Wallahi Allah na rantse da Alƙur’anin nan Kwankwaso yafi Atiku da Tunubu nagarta —Dr Hussain

Wani matashin malamin addinin Islama a jihar Kano mai suna Dr. Hussain Kano ya ɗaya Alƙur’ani ya rantse kan cewa “Wallahi Allah Kwankwaso yafi Atiku da Tunubu nagarta irin ta siyasa

Budaddiyar Wasika zuwa ga Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa @Sen Abdullahi Adamu da dukkan Manyan Shuwagabannin Jam’iyyar APC,

Bayan Dubu Gaisuwa tare da Fatan Alkhairi gare Ku baki Daya,

Ina Roko tare da fatan don wanda zai iya Kai Sakon nan nawu zuwa ga wadanda ya kamata Su sani zai taimaka ya isar Min da Shi,

Suna Na Hamis Nababa dake Garin Malumfashi jahar Katsina a yanzu haka Ni Councilor ne a Karkashin Jam’iyyar APC,

Ina Son inyi amfani da Kafar Sada Zumunta ta Social media domin Kira ga Shuwagabannin Jam’iyyar Mu ta APC a Matsayi Na na cikakken Dan-Jam’iyyar APC mai Tsananin Kishin Ta,

Bayan duk Aiyukan Alkhairin da Jam’iyyar APC tayi a tsawon Shekaru 7-8 Yau Gwamnan Babban Banki Nigeria yana neman Rusa Su cikin Kasa da Watanni Ukku,

Duk irin Dalilin da Emefele yake da Shi nayi Chanji ya kamata a kalli yanayin da ake ciki da Lokacin da Muke ciki a Yanzu,

Abinda yasa nasa Jam’iyyar APC saboda Gwamnatin ta Ce duk wani mai Kujera ko wacce iri Ce Albarkar Jam’iyyar yake Ci,

Idan har Yan-Majalisu Sun zura IDO, Jam’iyya Bai Kamata ta Zura IDO Emefele ya Rusa ta Ba,

YAU Alumma Sun ajiye Komi sun tare Banki a dai-dai lokacin da aketa fama da Su domin Amincewa da Aiyukan Alkhairin da wannan Jam’iyya ta Shinfida Su daure Su sake Zaben Ta,

Kada Jam’iyyar APC ta Mance cewa akwai tabbacin AGENDA mai Inganci cewa Mabiya wani ADDINI zasu taimaki wani Dan-Takarar Shugaban Qasa daya fito daga Kudancin Nigeria kota halin K’a-k’a domin ya Kai Labari,

Idan muka Kallin wannan Chanjin Kudin yafi illa a Arewacin Nigeria,

Lallai ya zama Wajibi ga Shuwagabannin Jam’iyyar APC Su Hanzarta ganin Shugaban Qasa domin nuna mashi illar wannan WA’ADIN da aka sama Chaji,

Saboda Mu anan AREWA ya taba Tattalin Arzukin Mutanen Mu gaba Daya 100%,

Yau duk inda Ka Shiga Lungu da Sako wannan Matsalar itace abinda ya Addabi Zukatan Mutanen Mu,

Ita Kuma taken Jam’iyyar APC shine Jam’iyyar TALAKA”Watau Jam’iyyar da aka kafa domin Kare Maradun Alummar Nigeria”

ALLAH yasa wannan Wasika tawu taje hannun wadanda suka dace taje Hannun Su sannan suyi Nazari tare da Daukar Matakin daya dace,

Views: 22

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *